Wednesday, 16 January 2013

HUJJOJIN MAULIDI


Dr. Ibrahim maqari Zaria Bismillahirrahmanirraheem...
HUJJOJIN MAULIDI...
1- kalman almaulidu a
littafan musulunci gaba
daya farkon wanda ya fara
ambatonsa da nufin lokacin maulidin Annabi ko
wurin da aka haifi Annabi
shine Abdullahi ibn
muhammadd ibn
abdulrahman mawallafin
littafin akhabaru makkata, ya rayu zamanin su
ahmadu bin Hambal har
ma ya girme shi, ya rasu
223Hijr... Ya amabata da
nufin bigiren da aka haifi
SHUGABA S.A.W kuma ya fadi girman wurin... 2- ibn jubayr ya rasu hijira
nada shekara 615Hjr ya
ambaci maulidi a cikin
rihlansa ya ce duk ranar
litini na watan rabiu auwal
ana bude shabbakin Annabi mutane na shiga
suna tabarruki da raudhan

har watan ya kare... 3- ibn kathir a cikin bidaya
wannihaya, 4-alhafiz suyuti... 5- wanda ake jingina
farkon maulidi zuwa gare
irin yanda muke yi shine
almalikul muzaffar... 6-imamu abu shamata
662Hjr... malamin duk
malaman zamanninsa
saboda shine malamin
imam nawawi ma, ya
rubuta wani littafi (alba'ithu ala inkaril
bida'I...) A cikin wannan
littafin ya ambaci cewa fa
akwai wani abun da abu
shamata yake yi yace ba
bidiah bane, in ma bidiah ne to hasana ne, ya ambaci
maulidi... Yace hujjanshi
kuwa shine saboda yana
shigar da soyayyar Annabi
a cikin zukata... Saboda
fadin SHUGABA (ku tarbiyantar da yayanku
akan abubuwa uku...son
Annabi, son ahalil bayti, da
tilawan Qurani) 7-muhammad bin
abdullahi ibnul Hajj, a cikin
almadkhalu ya fadi cewan
maulidi abu ne mai kyau,
saboda SHUGABA yace
(yana azumin litini ne saboda ranan aka haife shi)
a ilimin ibnul hajji kenan... 8- Ibn Taymiya 727hijr
yace maulidin Annabi abu
ne mai kyau gwargwadon
niyyan me yi, ya fada a

wuri biyar a cikin iqtida'ul
siratil mustaqim... 9-ibn abbas almisri yace
maulidin na da kyau
hujjanshi kuwa shine
saboda sayyidna abubakar
har fata yake yayi wafati
ranar haihuwan Annabi ranar litini..hadisin na cikin
musnad na imam ahmad
da ibn hibban etc... 10-ibn batuta 772Hijr yace
ya ga ana yi a madina da
makka ya ce duk in watan
yazo ana ciyar da abinci
ana girmama sharifai ana
basu manyan hadaya har watan ya kare... 11-alhafiz ibn hajar
alasqalaniy yace maulidi
abu ne mai asali mai hujja
dalili kuwa shine abunda

Annabi yace da ya tarar
ana azumin ashura saboda murnar tsiran Annabi musa
to ashe samuwan SHUGABA
abun ayi murna ne... 12-shamsuddeen sahawy
902Hijr yace maulidi nada
kyau sabooda Allah yace
(ku aikata alkhairi) kuma
duk abunda ke maulidi
alkhairi ne 13-imam sayuti 911Hijr
yace maulidi nada kyau
saboda Annabi har yanka
ya kara ma kansa bayan
kuma ya san anyi mashi... 14- imam zakariyal ansari
1065Hijr yace maulidi nada
kyau saboda hadisin matan
nan da tace idan SHUGABA

ya dawo daga yakin
khaibara zata kada duffu a gaban SHUGABA, Annabi
yace ki cika bakacenki, yace
to wannan murna ne da
dawowan Annabi ashe
zaka iya muurna da
zuwanshi duniya, 15 imam allusi mawallafin
ruhul ma'ani shima yace ya
samo hujjan maulidi
saboda Allah na karanta
ma Annabi kissoshin
annabawa saboda a kwantar da hankalinshi to
ya kuma kissan SHUGABA? 16-imam qastalaniy mai
sharhin bukhari yace
maulidi nada kyau Allah
saboda yace (qul bi
fadlillahi wa bi rahmatihi fa
bi zalika fal yafrakhu...) 17 Shiekhul Islami Wa
Sa'adatul Anami Sheikh
Ibrahim Niass yayi fatawa
biyu akan maulidi na farko
shehu ya taba fadan qul bi
fadlillahi a matsayin hujja, se kuma fatawan sa na
kansa R.A da aka
tambayesa se yace RASHIN
HUJJAN domin akwai
abunda yafi karfin hujja
saboda ba'a neman rana da rana tsaka... To duk
mutumin da ranar
haihuwan Annabi ya
zagoya be yi murna koda a
zuciya bane to be da IMANI.

7 comments:

  1. Allah ya kare ka daga dukkan sharrin mai sharri dan Darajar Fiyayyan Halitta (saw).

    ReplyDelete
  2. Allah ya Qarawa shehi lafiya, da nisan kwana, da hazaqa, Allah dan lsar ANNABI MUHAMMADU Ka Qarawa SHEHI Kusanci da Fiyayyan Halittah (saw).

    ReplyDelete
  3. Allah ya Kara daraja da fahimta. Allah ya kuma saaka da alkhairi

    ReplyDelete
  4. Allah ya kara hikima da fadaha alfarmar Muhammad Rasulullah S. A. W

    ReplyDelete
  5. Allah yayi riko da hannunka ya Sayyidi

    ReplyDelete
  6. Allah ya kara lafiya ya kare ka daga mahassada

    ReplyDelete