"""""""""SALATIL FATIH"""""""""""
.............................. .............................. .............
An karbo daga Sayyadina jabir dan Abdullahi
Allah ya kara masa yarda yace, wata rana nace
da Manzon Allah (S) uwata da ubana fansar ka
ya Rasulullahi, gaya min farkon abin da Allah
ya halitta kafin ya halicci komai. Sai Manzon
Allah (S) yace, ya jabir Allah ya Halicci hasken
Annabin ka daga hasken zatin sa kafin ya
halicci komai. Ya sanya wannan haske yana
kewayawa da kudurar sa yadda Allah ya so. A
wannan lokaci babu Allon Lauhil Mahfuz babu
Alkalamin Qudra babu Aljanna babu wuta ba
wani Mala'ika ba sama ba kasa ba rana ba
wata ba Aljani ba Mutum. Yayin da Allah Mai
Girma da buwaya yayi Nufi ya halicci halitta
sai ya raba wannan haske Izuwa kaso hudu.
Daga kaso na farko ya Halicci Alkalamin Qudra.
Daga kaso na biyu ya halicci Allon Lauhil
Mahfuz. Daga kaso na uku ya halicci Al'arshi.
Kaso na hudu ya sake raba shi izuwa kaso na
hudu. Daga kaso na farko ya halicci Mala'ikun
da suke dauke da Al'arshi. Daga kaso na biyu
ya halicci kursiyyu. Daga na uku ya halicci
sauran Mala'iku. Kaso na hudu ya sake raba
shi Izuwa kaso hudu. daga kaso na farko ya
halicci Sammai. Daga kaso na biyu ya halicci
kassai. Daga kaso na uku ya halicci Aljanna da
wuta. Kaso na hudu ya sake raba shi Izuwa
kaso hudu. Daga kaso na farko ya halicci
hasken maganah Muminai. Daga kaso na biyu
ya halicci hasken zukatan su, watau hasken
sanin Allah (Ma'arifa). Daga kaso na uku ya
halicci hasken kawunan su, wato hasken
kadaita Allah (Tauhidi)
La'ilaha'illallahu Muhammadur rasulullahi
(S.A.W).
.............................. .............................. ............................
KU SAURARA MASOYA ANNABI (S.A.W)
.............................. .... MAULUD NABIYI (S.A.W)
DOLE .............................. ...........
.............................. .............................. ............................
KU SAURARA MASOYA ANNABI (S.A.W)
.............................. .... MAULUD NABIYI (S.A.W)
DOLE .............................. ...........
KU SAURARA MASOYA ANNABI (S.A.W)
..............................
DOLE ..............................
Allah ya saka da alkhairi
ReplyDelete