Saturday, 12 January 2013

AHLIL BAITI

SUWANENE MASOYA AHLUL-BAITI na 3

1.
Al Aswadu xan Wahabu, ya musulunta, ya abokanci Manzon Allah (SAW), ya kuma ruwaito Hadisai daga gare shi.
2.
Abdullahi xan wahabu: ya musulunta ranar da aka ci garin Makkah.
3.
Umaru xan Wahabu: Ba cikakken labarinsa.
4.
Abdu Yagusa xan Wahabu: Shi ne mafi shahara daga cikin kawunnenManzon Allah (SAW). Bai riski Manzanci ba. Daga cikin zuri'arsa, akwai Al-Aswad xan Abdu Yagusa -ya mutu mushiriki, yana kuma mai tsananin tozartawa ga Manzon Allah (SAW). Sai dai ya haifi `ya'ya Musulmai, waxanda su ka abokanciManzon Allah (SAW) su ne; Abdurrahman da Khalidatu. Haka kuma ya na da xa mushriki mai suna, Arqamu xan Abdu yagusa, shi kuma wannan yana da xa mai suna Abdullahi xan Arqamu, wanda ya musulunta, ya abokanci Manzon Allah (SAW).

5.
Khalafu xan Wahabu: Yana da xa mai suna Al-Aswadu xan khalafu, sahabi ne, kuma ya yo ruwaya daga Manzon Allah (SAW).
Haka kuma Amina tana da `yan'uwan haihuwa mata, guda huxu(4) da suka haxa da:

1.
Fakhita `yar Amiru
2.
Furai'atu `yar Wahabu
3.
Uqailatu `yar kumainu
4.
Ummu Abdin, mahaifiyar Abdullahi xan Mas'ud
Tabbataciyar magana dai ita ce, dukan matan nan, danginta nedaga qabilar Bani Zuhrah dangin mahaifinta, amma ba abokan haihuwarta ba ne. Sai fa Uqailatu `yar kumainu, ita kam, `yar'uwar Aminatu ce ta wajen uwa, amma ba su haxa uba ba. Akan haka, ita ce Inna ta ainihi ga Manzon Allah (SAW).

1.5 Matan Manzon Allah (R.A)
Manzon Allah (SAW) ya auri mata goma sha xaya (11) a rayuwarsa.
1.
Khadijatu `yar Khuwailidu xan Asadu xan Abdul-Uzza xan Qusayyu: Macce ta farko a Musulunci, Uwar gidan Manzon Allah (SAW), Uwar `ya'yansa gaba xaya in ban da xan autansa Ibrahim. `Yar uwarsa ce ga zumunta, domin Qusayyu, kakanta na uku shi ne kakansa na huxu. Ta rayu tare da Manzon Allah (SAW), ita kaxai, a matsayin matarsa, tsawon shekaru ashirin da biyar (25), bai yi ma ta kishiya ba har Allah ya cika ajalinta. Ta taimaka ma Manzon Allah (SAW) matuqa, kuma ya kasance ya na daranjanta ta, ya na yaba ma ta. Kuma a lokacin da ta rasu ya yi baqin ciki ainun, sannan ya kasance ya na kyautata ma aminnanta a bayan rasuwarta.

2.
Saudatu `yar Zam'atu: Ita ce amaryar Manzon Allah (SAW) ta farko bayan rasuwar uwargidansa Khadijah, ta zauna tare da shi tsawon shekara Uku (3), ita kaxai. Da ya ke Saudatu dattijuwa ce, daga baya sai ta yafewa Nana A'ishah kwananta a wurin Manzon Allah (SAW), don ta san zai yi farin ciki da haka, ta na neman yardarsa.
3.
A'ishatu `yar Abubakar Siddiqu : Manzon Allah (SAW) ya auri Sayyada A'ishah, a cikin watan Shawwal, shekara ta tara (9), bayan da Allah ya nuna masa wannan auren a cikin mafarki in daya ga Jibrilu (AS) xauke da ita A'ishahr a cikin wani kyakkawan qyalle na alhariri, ya na ce masa: ga matarka. Nana A'ishah ta ci gaba da zama tare da Saudatu wasu tsawon shekaru uku kafin Manzon Allah (SAW) ya auri Hafsah`yar Umar. Ita kaxai ce budurwa daga cikin matansa kuma ya kasance, ya na matuqar qaunarta fiye da sauran matansa. A dalilin haka ne munafukai su ka shirya mata qarya, sai alqur'ani ya sauko daga wurin Allah ya na wanke ta. Ta yaxa ilmi mai tarin yawa da albarka a cikin shekaru kusan hamsin (50) da ta yi bayan Manzon Allah (SAW).
4.
Hafsatu `yar Umar xan Khaxxabi: Manzon Allah ya aure ta, a cikin shekara ta Uku (3) bayan hijira. Kamar yadda ta ke bi ma Nana A'ishah ga auren Manzon Allah (SAW), haka ma it ace ta ke takara da ita, a wajen farin jininta da quruciya.
5.
Zainab `yar Khuzaimah al-Hilaliyyah: Ita ce ake yi wa laqabi da Uwar talakawa, saboda yawan sadakarta. Manzon Allah (SAW) ya aure ta, da wata biyu ko Uku, Allah ya yi mata rasuwa.
6.
Ummu Salamata, Hindu `yar Umayyata, Baquraisha ce, Makhzumiyyah. Ita ce wadda ta ga Manzon Allah tare da Mala'ika Jibirilu, shi Jibirilun yana cikin siffarwani kyakkyawan saurayi daga cikin sahabbai ana kiransa Dihyatu.Ta na daga cikin mata masu hankali da ilmi. Ita ce ma ta lurar da Manzon Allah (SAW) game da wata dabara da zai jawo hankalin Sahabbansa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar ta ci nasara sosai, ta kuvutar da musulmi daga faxawa cikn hushin Allah da manzonsa.
7.
Zainab `yar Jahshu `yar Umaimatu `yar Abdul Muxxalibi. Allah (SWT) ne ya shirya aure tsakaninta da Manzon Allah (SAW) a shekara ta uku ko kuma ta biyar bayan Hijira. Kuma Allah ya xaura auren, ya ba da shelar haka cikin alqur'ani. Annabi kuwa ya yi mata walima qasaitacciya. Ta na da saurin fushi da saurin hucewa. Duk ta fi matan nannabi (SAW) yawan qasqantar da kai ga Allah da yawan ayukkan neman lada bisa ga shedar kishiyarta Nana A'ishah.
8.
Juwairiyyatu `yar Harisu: Manzon Allah (SAW) ya aure ta bayan yaqinda ake kira Muraisi'u, a cikin shekara ta biyar ko shida, bayan hijira. Kuma a sanadiyyarta ne musulmi suka `yanta bayi xari, daga qabilarsu ta Banul Musxalaq, su kuma a dalilin haka duk su ka musulunta.
9.
Ummu Habibah `yar Abu-Sufyana (Sarkin Makka). Sunanta na yanka shi ne; Ramlatu. Tana kuma daga cikin matan farko da suka yi hijira zuwa Habasha, in da mijinta ya rasu ya na musulmi. Sa'annan Manzon Allah (SAW) ya aure ta. Ta kasance mai yawan tsentseni da ibada da girmama Manzon Allah (SAW). A lokacin halifancinsa, qanenta Mu'awiyah ya kasance ya na matuqar darajanta ta, don haka ne ma ake ce masa “kawun Mummunai” saboda `yar uwarsa uwar Mummunai ce da nassin alqur'ani.
10.
Safiyyatu `yar Huyaiyu: Manzon Allah (SAW) ya aure ta, a cikin shekara ta shida bayan hijira. Kuma tana daga cikin zuri'ar Haruna xan Imrana, xan'uwan Annabi musa (AS). Mace ce mai haquri na natsuwa matuqa. Daga aurenta ne aka samu hukuncin namiji ya `yanta kuyangarsa, kuma yace ita xin kanta ce sadakin aurenta. Haka ne ita ya yiwa Juwairiyyah.
11.
Maimunatu `yar Harisu Al-Hilaliyyah: ita ce `yar autan matan Manzon Allah (SAW). Ya aure ta ne a cikin shekara ta bakwai bayan hijira, ya yi biko da ita a wani wuri da ake kira “Sarfu” lokacin da ya ke tafiya don ramka Umrarsa da bai samu yi ba a lokacin Hudaibiyyah. Nana A'ishah ta ba da sheda akanta ta na cewa, duk ta fi mu taqwa da kuma sada zumunta.
1.6 ` Y a'yan Manzon Allah (SAW) da jikokinsa m aza da mata:
Manzon Allah (SAW) ya haifi `ya'ya bakwai (7) Uku Maza, da suka haxa da:-
1.
Al-qasim : Shi ne xan farin, kuma da shi ne ake yi wa Manzon Allah (SAW) alkunya.
2.
Abdullahi : (ana yi ma sa laqubba biyu: Axxayibu da Axxahiru)
3.
Ibrahim : shi ne xan autan Manzon Allah (SAW).
Sai huxu (4) mata, da suka haxa da:
1.
Zainab: Ita ce babba a cikin mata. Ta auri Abul Asi xan Rabi'u daga qabilar Banu Umayyah, waxanda sun haxa zuri'a da Manzon Allah (SAW) a kakansa Murratu xan Ka'abu.
2.
Ruqayyatu: Ta auri Sayyiduna Usman (RA), Shugaban qabilar Banu Umayyah a lokacinsa. Ta rasu wajen naqudar xanta Abdullahi, a daidai lokacin da su ka fita tare da mijinta wajen yaqin Badr. Wannan ma shi ne daliln da ya sa SayyidunaUsman bai samu yaqin Badr ba, domin jinyarta a hanya. Amma Annabi (SAW) ya raba ganimar da shi, abin da ya ke nuna sun samu ladar yaqin da shi da matarsa.
3.
U mmu Kulsum : Ta auri mijin yarta Sayyiduna Usman, daga qabilar Banu Umayyah. Amma ba su samu haifuwa ba, har ita ma Allah ya karvi rayuwarta.
4.
F aximatu : ita ce `yar autar xakinsu, kuma mai bi ma xan autangidan bakin xaya, shi ne Ibrahim. Ta auri wanta Aliyu xan Abu xalib aqarshen shekara ta biyu, ta haifi `ya'ya biyar da shi kamar yadda za mu faxa a nan gaba kaxan.
Allah (SWT) ya ambaci waxannan `ya'ya mata na Manzon Allah, a xunqule, inda ya ce:
� (59) � [ ].
(ya kai Annabi ! ka ce wa ma ta na urenka da `ya'yanka mata, da matan muminnai su kusantar da qasa dag a manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauqi ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah ya kasance mai gafara mai jinqai)
[Suratul Ahzab : 59]
Waxannan `ya'ya na Manzon Allah (SAW) guda bakwai, duk Sayyidah Khadijatu ce ta haife su, sai fa Ibrahim, wanda mahaifiyarsa ita ce; Mariyah al-qibxiyyah. Uku daga cikin `ya'yan Manzon Allah (SAW) xin nan, mata, wato; Faximatu da Zainab da Ruqayyah sun kai fagen yin aure da haihuwa.
a.
Faximatu `yar Manzon Allah (SAW) ta haifi:-
1.
Hassan(Ya haifi zuri'a mai yawa)
2.
Hussaini(Shi ma zuri'arsa ta yaxu)
3.
Muhsinu (ya rasu yana qarami sosai)
4.
Ummu Kulsum, wadda ta auri Sayyiduna Umar ta Haifa ma sa; Zaidu da Ruqayyah. Bayan da ya rasu sai ta auri `ya'yan Amminta guda uku; Aunu da Muhammadu daAbdullahi `ya'yan Ja'afaru xan Abu xalib, xaya bayan xaya, qarshe ta rasu hannun Abdullahi xan Ja'afarusai kuma aka ba shi `yar'uwarta Zainab, suka haifi `ya'ya da dama.
5.
Zainab - al Kubra (wadda mu ka faxa a sama).
b.
Zainab `yar Manzon Allah (SAW) ta haifi:-
1.
Aliyu, da
2.
Umamatu: Mahaifinsu shi ne Abul Asi xan Rabi'u daga qabilar Banu Umayyah. Umamatu qarama ce a zamanin Manzon Allah (SAW), ya kan xauke ta idan ya na sallah. A lokacin rasuwar Nana Faximatu ne ta yi wa mijinta Sayyiduna Ali nuni da auren Umamatu xiyar yarta. Hakan kuma aka yi. Shi kuma a lokacin rasuwarsa sai ya yi ma ta nuni da ta auri xan uwansu Mugiratu xan Naufalu xan Harisu xan Abdul-Muxxalibi, kuma hakan aka yi. Ta haifu da shi amma zuri'arsu ta qare, bat a yaxu ta.
c.
Ruqayyatu `yar Manzon Allah (SAW) ta haifi :-
1.
abdullahi xan Usman xan Affan (ya rasu yana qarami sosai)
Wannan shi ne bayanin waxanda Ahlulbaiti su ka qunsa a wurin Ahlus Sunnah. To, a wurin Rafilawa abin ya banbanta, domin kuwa Ahlulbaiti a wurinsu su ne, mutanen kisa'u kawai. Sun kuma yi ittifaqi a kan cewa matan Manzon Allah (SAW) ba su daga cikin Ahlulbaiti .

Hujjar Rafilawa, a kan wannan matsayi, ita ce faxar Allah (SWT)
� � ( :23).
“Kace, “ Ba ni tambayarku wata ijara a kansa, face dai
soyayya ta cikin zumunta” [Surar shura : 23].
Su kace, wai an tambayi Annabi (SAW) ma'anar wannan aya! sai ya ce Allah na nufin: Aliyu (RA) da Faximatu ne, da `ya'yansu Hassan da Hussaini.
A fili ya ke cewa, sun kauce ma gaskiya, domin kuwa wannan aya tana cikin Suratus Shura ne, wadda ta sauka a Makka kamar yadda tarayyar masana asirin saukarsurorin Al-qur'ani suka tabbatar, kafin zancen auren Ali da Faximatu, ballantana haifuwar Hassan da Hussaini. To, ta yaya Manzon Allah (SAW) zai fassara waccan aya, da cewa tana nufin son Al-Hassan da Al-Hussaini, alhali ba'a ko yi auren mahaifansu ba ballantana a haife su?!
Xan Abbas, shahararren masanin al-qur'ani wanda kuma ya fi gaba xayan Ahlulbaiti Ilmi, sai fa Ali (RA) ya fassara wannan aya da cewa: zumuncin da Allah ke nufi a cikin ayar, shi ne gaba xayan dangin Annabi (SAW) kuma babu wani gida daga cikin gidajen quraishawa face Manzon Allah (SAW) na da dangantaka da su ta wajen wasu kakanninsa. Saboda haka ne ma,
Ibnu Taimiyya ya hukuntar da zamanwancan Hadisi, da suka kafa hujja dashi, zuqi ta mallau. Haka ma Ibnu Hajar ya raunana shi.
Haka nan kuma daga cikin hujjojinsuakwai ayar mubahala, wadda a cikinta Allah (SWT) ya ke cewa :
� (61)齕 ].
“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abinda ya zo maka daga ilmi, to ka ce : “ku zo mu kirayi `ya'yanmu da `ya'yanku da matanmuda matanku da mu kanmu da ku kanku, sa'a nnan kuma mu sanya la'anar Allah a kan maqaryata”. [Surar Ali Imrana : 61]
Su ka ce tun da ya ke, a lokacin da Allah ya saukar da wannan aya ya naumurnin Manzonsa da ya yi mubahala da kafirai, ya kawo danginsa su kawo nasu, ba'a ga Manzon Allah (SAW) ya kira kowa basai Ali da Matarsa da `ya'yansa. Wannan ya nuna kenan ba shi da wasu dangi in ba su ba.

To, amma kuma ai ayar ta faxi da matanmu da matanku. Gaskiyar magana ita ce, ana nufin ya kira makusantansa, kuma ba lallai sai dukkansu ba. Don haka ne sai manzon Allah (SAW) ya gayyato Ali daga cikin danginsa Maza, Ya kira Faximatu daga cikin mata, Ya kira Hassan da Hussaini daga cikin `ya'ya.To, wane ne ya ce, wanda ba'a kira a rannan ba an kore shi daga cikn dangin Manzon Allah (SAW) da makusantansa, kuma har matansa ba iyalansa ba ne tun da bai kira su ba?
Sauran `ya'yan Manzon Allah (SAW) su shida (6), da zuri'arsu, da matansa goma sha xaya (11) da muka lisafa duk `yan shi'a sun kore su
daga zama Ahlulbaiti

No comments:

Post a Comment